Spread the love

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce magabacinsa, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, yana shirin komawa jam’iyyar APC don yin takarar shugaban kasa a 2023.

Da yake karbar shugaban jam’iyyar PDP na Kano Dakta Rabi’u Sulaiman Bichi, zuwa APC, Ganduje ya ce babban burin Kwankwaso shi ne ya tsaya takarar shugaban kasa.

Ganduje, yayin da yake kwatanta Kwankwaso a matsayin “ɗan siyasa mara-kima ‘, wanda bai san komai ba a fagen siyasa, ya ce magabacinsa“ baya son wani mutum ya haskaka, kan shi kawai yake soq “.

“Na san Kwankwaso fiye da kowane mutum. Shi wani irin mutum ne wanda yasan komai, ya fi kowane mutum sanin shi kuma mai son kai ne.

Duk abin da mutumin nan ya ce ka yi zai amfane shi ne ba kai ba.

“Na san duk dabarun siyasarsa, yaudara da wulaƙancinsa amma na jure shi tsawon shekarun da muke tare.

Ba zai taɓa gode maka saboda abin da ka yi masa ba, babba ko ƙarami.

“Lokacin da muka tsaya takara a 1999, ‘Wallahi’, ni ne maigidansa saboda na ni biya kuɗin buga Fastocin siyasarsa kuma na tattara mutane daga shiyyoyi 44 na jihar Kano.

A zahiri, Kwankwaso bai ci zaben fidda gwani a 1999 ba, na ci zaben, amma aka sulhunta mu.

“Ba Kwankwaso ya ba ni mukamin mataimaki ba a wa’adin mulkin sa na farko. Haka na ta yi masa biyayya a gare shi tsawon mulkinsa na farko.

Lokacin da aka naɗa shi minista, ya gayyace ni in zama mai ba shi shawara na musamman. Da farko dai, na ki, amma da ya nace sai karbi bukatarsa, ”in ji Ganduje.

Gwamnan ya kuma tuna cewa lokacin da Kwankwaso ya dawo wa’adinsa na biyu a shekara ta 2011, ya gayyace shi ya zama mataimakinsa.

Sannan, ya yi takaicin cewa duk da cewa suna PDP a lokacin, amma Kwankwaso ya nace cewa ya kamata su sauya sheka zuwa APC don su ba shi damar aiwatar da burinsa na shugaban kasa.

“Bayan na ci zabe, na roki Kwankwaso ya bani Sakataren Gwamnatin jiha na mulkin (SSG) da Akawun jiha (AG) tare da Sakataren Yada Labarai da sauran jami’ai. Na kuma nemi ya halarci bikin rantsar da ni amma ya ƙi. Madadin haka sai ya ce zai je Kaduna. Na kira mutumin nan sau tara don gano ko ya iso Kaduna lafiya bai dauki wayata ba, ”inji shi.

A nasa jawabin, Bichi ya ce sun yanke shawarar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ne bisa gayyatar da Ganduje ya yi wa ‘yan adawa da su hada hannu da gwamnati wajen ciyar da jihar gaba.

“Mun yi imani da cewa gwamna Abdullahi Ganduje da gaske yake wajen bunkasa jihar, shi yasa muka yanke shawarar hada hannu da shi domin ciyar da jihar mu gaba. “Don haka a yau muna amsa kiran Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Ganduje.

Ya ce ci gaban kasa da muke gani a duk faɗin jihar da sauran manufofi na mutumtaka kamar kyauta da tilasta karatun firamare da sakandare wasu manyan dalilai ne da suka.isa mu amsa gayyatar gwamna, ”ya kara da cewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *