Spread the love

Sanata Kashim Shattima mai wakilta Borna ta tsakiya a majalisar dattijan Nijeriya tsohon gwamna ne da ya jagoranci jihar shekara takwas, ya yi magana da yawa a taron da jaridar daily trust ta gayyace shi kan lamurra da dama har da maganar boko haram da gangancin da tsoffin gwamnoni ke yi bayan sun bar mulki su tsayin daka sai sun juya wadanda suka gade su don kawai sun yi masu gatan daura su saman mulki.

Sanata ya ce shi da gwamna Zulum suna da kyakkyawar fahimta da mutunta juna, da zaran ka bar kujerar gwamna kamata ya yi ka girmama kanka ka bari wanda ya gade ka ya yi aiki.

Ya ce shi da Zulum sun yarda da haka suna aiki don ciyar da Borno gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *