Spread the love

Daga Comr Abba Sani Pantami

Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce kamata ya yi a ce sai nan da shekara 50 ne Shugaba Muhammadu Buhari zai mulki Najeriya, domin ta haka ne za a fi ganin tasirin mulkinsa.

Shettima, wanda shi ne ke wakiltar Borno ta Tsakiya a majalisar dattawa, ya shaida wa Daily Trust cewa “burin da ‘yan Najeriya suka dora kan mulkin shugaban ya yi yawa”.

“Wani lokacin sai na ji kamar cewa nan da shekara 50 ne ya kamata Buhari ya mulki kasar nan saboda irin abubuwan da wasu ke gani a matsayin gazawarsa su ne ainahin nasarorinsa da kwarewarsa,” a cewar Sanatan.

Ya kara da cewa “Buhari yana nada mutum a kan mukami, ya kuma sakar masa mara ya yi duk abin da ya ga ya dace tare da bin ka’ida da sanin ya kamata; amma a tsarin Najeriya hakan ba ya yiwuwa”.

Sanata Shettima ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su jinjinawa Shugaba Buhari kan yadda yake farfado da tattalin arzikin kasar.

“Wannan na daya daga cikin bangarorin da wasu ba sa so su jinjinawa shugaban duk da nasarorin da ya samu saboda tattalin arziki ya tabarbare matuka lokacin da ya zo.

Alal hakika ya farfado da tattalin ariziki. A karon farko ga shi muna fadada kasafin kudinmu, ana tunkarar manyan aikace-aikace na ci gaban kasa”.

Ya kara da cewa “ina ganin ba ma jinjina masa kamar yadda ya cancanta”.

Tsohon gwamnan na Borno ya kuma yi magana a kan dimbin kudaden da wasu tsaffin gwamnoni ke karba a matsayin fansho, da dalilin da ya sa ya goyi bayan Farfesa Babagana Zulum a matsayin magajinsa da batun ‘yan matan Chibok da sauransu.

Duk waɗan nan kalmomi ya furta su ne a hirar da ya yi da jaridar daily trust.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *