Spread the love

Hukumar kula da yara ta duniya UNICEF mai ofis a Kano babban jami’inta Maulid Warfa ya bayyana kididigar kiyon lafiyar yara a Nijeriya abin kulawa ce.

A cewarsa sama da yara dubu 250 ne suka mutu a Nijeriya a farkon rayuwarsu a duniya.

Ya yi kalaman ne a taron karawa juna sani a Kano ya ce kididigar ta sanya kasar zama ta biyu a duk duniya kamar yadda rahoton 2017 ya nuna.

Akwai bukatar duba halin da yara suke ciki kar abari a tafi haka.

Ya ce wannan abin da ba a yi tsammani ba ne mafi yawan yaran da ke mutuwa ba su isa haihuwa ba ko wasu matsaloli wajen haihuwa, ko cirutoci na maleriya da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *