Spread the love

Annobar cutar Lassa ta watsu jihohin Delta da Enugu da wasu jihohi guda bakwai tun farkon shekara da cutar ta fara jaridar daily trust ta samu bayanin.

Cutar ta kashe mutane 16 a Ondo, 3 a Kano, Edo da Delta mutum daya-daya.

Daruruwan mutane ana kule da su musamman a jihohin Kano da Ondo.

Mutuwar na karuwa daidai da yaduwar cutar, ana kokarin kange mutanen da cutar ta shigo.

Hanyoyin kariya daga cutar Lassa kamar yadda masana suka fadi kowane mutum ko iyali su tabbatar da tsaftarsu haka kuma su tabbatar da gidajensu ba Bera kuma su rika rufe abincinsu da abin shansu da kyau.

Masu sayar da abinci saman hanya su rika rufe shi, duk wanda zai taba maras lafiya ya sanya safar hannu, kamar yadda babban jami’i a kula da cutar a Asibitin Abuja Dakta Ogugua ya fadi, ya kuma shawarci mutane da zaran sun kamu da Zazzabi su tafi Asibiti don ba kowane zazzabi ne na Maleriya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *