Spread the love

Shugaban PDP Na Jihar Kano Kuma Jigo ne Kwankwasiyya, Rabiu Suleiman Bichi Ya Koma APC

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano kuma babban na hannun daman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wato Rabiu Suleiman Bichi ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC.

Sauya shekar dai ya biyo ne kwana daya da yanke hukuncin shari’ar gwamnan Kano da kotun koli ta yi, inda ta tabbatarwa da Ganduje kujerar Gwamnan Kano.

Tun kafin kammala shari’ar PDP ta yi zama in da ta rushe shugabancin Rabi’u Bichi abin da bai gamsu da shi ba ya ce shi ne halattaccen shugaban.

Managarciya ta gan shi a wurin taron PDP na ƙasa da aka kira kwanan nan, sai g shi kuma ya bar jam’iyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *