Sama da mutum miliyan 60 ne ba su iya karatu da rubuta ba a Nijeriya

Hukumar samar da ilmi bai ɗaya ga manya da wadan da ba su yi karatu ba suna ƙanana ta ce sama da mutum miliyan 60 ne ‘yan Nijeriya ba su iya karatu da rubutu a cikin kowane harshe.

Sakataren zartarwa na hukumar Farfesa Abba Abubakar Haladu ya faɗi haka a Abuja a wurin tattaunawa kan ilmi.

Abubakar ya ce ƙalubalen da ake da shi na yaran da ba su zuwa makaranta, Nijeriya na ƙara zama a gaba a yawan marasa ilmi a tsakanin manya da matasan al’ummar.

Ya ce wannan yana cikin manyan abin da suka sanya ƙasar ba ta cigaba, miliyoyin mutane manya da matasa na cikin jahilci.

Ya ce Nijeriya na iya cimma muradun ƙarninta ne in mutanen ƙasar sun kaucewa duhun jahilci suna iya karatu da rubutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *