Mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya fahimci Almajirai ba bata-gari ba ne, rashin kulawar iyaye ne ta jefa su cikin halin da suke.

Ya yi kira ga malaman addinin musulunci dake Arewacin Nijeriya da su fito da wasu hanyoyi da za a shawo kan lamarin a yankin.

Sarkin musulmi ya yi wannan kiran ne a garin Minna na jihar Neja a lokacin da yake magana a madadin mutane daidaiku 100 da kungiyoyin sa-kai don karrama cibiyar yada addini(IET) a rawar da ta taka wurin samun fahimtar juna ga addinai.

Basaraken ya samu wakiltar Sarkin Kano Muhammad Sanusi ya ce mahaifan Almajirai da suka fita batunsu za su samu sakamako a nan duniya ko a wurin Allah ranar tashin kiyama.

Ya fahimci ana iya ciwo kan lamarin in aka bi hanyar da ta dace da kuma magance kalubalen da yaran suke ciki tsakaninsu da ilmi.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *