Spread the love

APC a ranar Litinin ta ce jam’iyarsu ba za ta yi yanda PDP ta yi ba duk da suna da hujjoji na nuna cewa tabbatar da nasarar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal abin mamaki ne da ba a yi tsammani ba. 

Sakataren yaɗa labarai na APC Malam Lanre Issa-Onilu, ya fitar da wannan bayani a  Abuja.

“Mun rasa gwamnan Sokoto ga PDP a hukuncin kotun ƙoli na yau.” 

Ya ce hukuncin ya zo mana ba zata kwatakwata ba mu yi tsammanin haka ba bisa ga hujjojin da muke da su. “Alhaji Aminu Tambuwa, gwamna mai ci yana saman kujerarsa ne kan ƙuri’a 342, amma akwai ƙuri’u sama da 30, 000 da aka soke, wannan abu ne da ba a yi tsammani ba ya yi nasara kotun ƙoli. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *