Spread the love

Kotun ƙoli ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Ahmad Aliyu na jam’iyar APC ya yi na ƙalubalantar zaɓen Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a matsayin gwamnan Sokoto a 9 ga watan Maris.

Hukuncin a gaba ɗayan alƙalan su biyar ƙarƙashin jagorancin Alƙali Sylvester Ngwuta, sun ce Aliyu ya kasa tabbatar da shedunsa gaban kotun ƙolin. 

Hukuncin wanda Alƙalanya Uwani Abba-Aji, ta karanta ta ce shedannun da Ahmad ya gabatar ba su da wani nauyi kamar yadda Tarabunal ba ta gamsu da su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *