Spread the love

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan ya yi zargin cewa jam’iyyar APC na shirin yin amfani da Kotun Koli wajen karbe iko a jihohin Sakkwato, Bauchi, Adamawa da Benue.

Jihohin hudu da ke ƙarkashin ikon PDP a Arewacin Najeriya a halin yanzu, wanda kuma kotun koli za ta yanke hukunci a kansu a farkon mako mai zuwa biyo bayan koke da korafe-korafen da jam’iyyar APC da ’yan takarar gwamnoninta ke yi a zabukan gama-gari na 2019 da aka gudanar.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Asabar da ta gabata, ya ce duk da wadannan farmaki da ake zargi, har yanzu PDP ba za ta girgiza ba, ta mai da hankali ga samun nasara.

Ya ce hukuncin da Kotun Koli ta yanke game da zaben gwamnan Imo a ranar Talatar da ta gabata ba shi ne karshe ba, PDP ta gano sabbin tsare-tsare da jam’iyyar APC da jami’anta suka yi don amfani da kotun kolin ta kwace wasu jihohin PDP.

Shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a madadin abokan aikin sa, ya yi Allah wadai da furucin PDP kan hukuncin kotun koli kan kujerar gwamnan Imo, inda ya ce hakika Jam’iyar PDP ba ta yi wa bangaren shari’a adalci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *