Spread the love

Injiniya Buhari Ahmed Dan warai dake karamar hukumar mulki ta Aliero Jihar Kebbi

Matashi ne da ya kware wajen kera abubuwa masu motsi inda acikin kere kerensa ya kera abubuwa da suke da mihimmanci ga rayuwa

Inda ya kera mota mai noman shinkafa da kanta tayi chasa tayi zafa da kanta

Haka kuma ya kera injimin chasar shinkafa

Da kuma Injin Dashen Albasa tare da na ban ruwa.
Injiniya Buhari Danwarai ya kera wata Na’ura da take nika Tumatur da Lemu, ta kuma nika Dawo(fura) ta mayar dashi fura da aka dama ya kuma niƙa ko markaɗa Kankana, da Abarba dama duk wani nau’i na ya’yan itace yanzu haka dai Injiniya Buhari yana cigaba da ƙera wani nau’in Injimin da bai baiyyana ko na minene ba inda yace sai ya karasa aikinsa ne zai yiwa Duniya bayanin aikin wannan Injimin
Inda yake sa ran halartar bukin kamun kifi na Argungu da za’ayi nan gaba ba da dadewa ba insha Allahu domin baje hajarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *