Spread the love


Al’ummar Jihar Zamfara musamman magoya bayan jam’iyar APC sun samu bayanai tare da Kalamai har ma da tattaunawa wadda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sani Ahmed Yariman Bakura ya bayyanawa manema labarai, cewar Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle yana dab da dawowa a jam’iyar APC  a jihar Zamfara.
Hakika wannan ba abun mamaki ba ne idan akace wannan bayani ya fito ne daga bakin tsohon Gwamnan zamfara Ahmad Sani Yariman Bakura, domin kuwa dukkan wanda yasan irin sabon salon siyasa “Me fuska biyu” da Yarima ya dauko yanzu a jihar zamfara zai ƙara tabbatar da wadannan kalaman sun fito ne daga bakin Yariman Bakura kuma ba zai yi mamaki ba.
Sai dai yana dakyau Yariman Bakura ya sani cewar yanzu al’ummar jihar Zamfara musamman magoya bayan jam’iyar APC tuni sun yi fatali da dukkan wani salo na siyasarsa, sun rungumi tsohon Gwamna Abdulaziz Yari a matsayin jigon jam’iyar APC a jihar Zamfara, ganin irin yanda yanzu tsohon Gwamna Yariman Bakura yake cikin dambarwar siyasa ta amfani da sabon salon siyasar hada  kai da jam’iyar PDP a zamfara wajen tarwatsa jam’iyar APC, da jigon jam’iyar  tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari, magoya bayan jam’iyar APC har ma da al’ummar jihar zamfara baki daya sun riƙe  rashin aminci na siyasa da rashin dattako da ya bayyana karara a fuskar tsohon Gwamna Yariman Bakura.
Duk bayan shirye-shirye da ƙulle-ƙulle wanda ake zargin Yariman da su na zama silar dukkan wasu matsaloli da jam’iyar APC ta fuskanta a zaben shekarar 2019 da ya gabata, tare da yin fuska biyu a siyasar zamfara da goyon bayan ‘yan tawaye na kungiyar G-8 don tarwatsa jam’iyar APC a zamfara a bangare daya wanda Yariman Bakura ya yi nasara a wannan karon.
Yanzu yana da kyau tsohon Gwamna Yariman Bakura ya kara sanin cewar dukkan al’ummar jihar zamfara har ma da yan jam’iyar APC a jihar ta Zamfara ba sa tare da duk wannan yunkuri nasa na dawowa da Gwamna Bello Matawalle zuwa jam’iyar APC, saboda wani boyayyen kuduri nasa, da kuma shirye shiryensa na takarar kujerar Shugaban Kasar Najeriya a zaben 2023 me zuwa da kudaden zamfarawa.
Hakika akwai mamaki a wani bangare ace irin tsohon Gwamna Yariman Bakura zai iya wani tunani a halin yanzu na yunkuri ganin cewar Bello Matawalle ya dawo jam’iyar APC a zamfara, duk da irin matsaloli da wahalhalun rayuwa wanda yau gwamnatin Bello Matawalle ta jefa al’ummar zamfara. Haka zalika Gwamna Matawalle wanda yanzu shi ma da kansa ya kasa jagorantar ‘yar karamar jam’iyarsa ta PDP a zamfara, ta ya ya Yariman Bakura yake tunanin dawowa da Matawalle APC ko kuma zai iya kula da irin jam’iyar APCn zamfara koma ya ciyar da ita gaba. Jam’iya wadda ta kunshi miliyoyin magoya baya da kuma jagorori masu dinbin yawa karkashin jagorancin hazikin Shugaba tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari.
Ko Yariman Bakura ya manta cewar shima Gwamna Matawalle ba zabensa al’ummar zamfara suka yi ba a matsayin Gwamnan zamfara, sai dai ya samu nasara ne daga hukuncin kotun koli akan kulle kulle wanda shi Yariman Bakura ake zagin ya hadakai da yan G-8 don kawarda APC.
Abun takaici ne ace dukkan irin zalunci da cin zarafi wanda gwamnatin Bello Matawalle take yiwa magoya bayan jam’iyar APC yau a jihar zamfara, wani mutum wanda yake kiran kansa dan jam’iyar APC irin Yariman Bakura ya amunta da kudurin ganin dawowa da Matawalle a cikin APC, sai dai idan da wani boyayyen shiri ne wanda ake zargin Yariman Bakura da fara kullawa na kokarin tarwatsa jam’iyar APC kamun zaben 2023, wanda al’umma jihar zamfara tuni suka kulla shiri kuma suke jiran zuwan lokacin zaben 2023 don kawarda gwamnatin PDP da Bello Matawalle daga jihar zamfara.
A halin da ake ciki yanzu a zamfara, alamu duk sun tabbatarda cewar Yariman Bakura ba ya duba daga maslahar mutanen jihar Zamfara ko cigaban zamfarawa, sai dai kudurinsa na ganin cewar ya dawo da Bello Matawalle zuwa APC don shirin amfani da kudaden gwamnatin zamfara wajen neman takarar Shugabancin Kasar Najeriya da Yariman Bakura ya ke nema yanzu ido rufe.
Ko baya ga wannan yunkuri na dawowa da Bello Matawalle a cikin jam’iyar APC da Yarima yake, akwai wani boyayyen shiri da ake zagin Yarima ya sa ke hadakai da Shugaban jam’iyar APC na kasa Adam Oshiomole don kawarda tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari akan zama Shugaban jam’iyar APC na kasa, bayan dukkansu sun fahimci tabbacin da bayanai na cewar dukkan masu fada aji a jam’iyar APC dama dattawan Najeriya sun bada goyon baya wajen tabbatarda tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari a matsayin sabon Shugaban Jam’iyar APC na Kasa don samun nasarar APC a zabukan shekarar 2023 me zuwa da ma bayan wannan lokaci
Abu ne wanda dukkan al’ummar jihar Zamfara dama Najeriya baki daya suka sheda cewar, tun kafuwar jihar zamfara shekaru fiye da 20 wanda suka wuce, ba wani Gwamna wanda ya taba samar da abubuwan cigaba kuma ya ceto zamfarawa daga irin halin kunchi da yunwa da fatara wanda gwamnonin baya suka jefasu a ciki tare da kaddamar da shiraruwan cigaban al’umma da har yanzu suke magana da kansu a madadin wanda ya aiwatardasu kamar tsohon Gwamna Abdul’azi Yari, dalilin haka yasa har gobe mutanen Zamfara suke mubayi’a ga dukkan wani tsari ko siyasa wadda Abdul’aziz Yari ya zo masu da ita a jihar zamfara ba tare da jayayya. Wannan yana daga cikin dalilai wanda yasa yanzu a kowace rana jagororin jam’iyar PDP har ma da kwamishinoni na gwamnatin Bello Matawalle suke cigaba da chanza sheka zuwa APC karkashin Jagorancin jagora Abdul’aziz Yari.
Tabbas har yau zamfarawa basu manta da irin gwamnatin zalunci wadda tsohon Gwamna Yariman Bakura ya gabatar akansu ba a lokacin gwamnatinsa, kuma har yau suna cigaba da rokon Allah akansa da irin kulle kullen sa ga jam’iyar APC a zamfara da kuma jagoran tafiyar Abdulaziz Yari. Sannan ba za su manta yanda Yariman Bakura ya yi amfani da maganar kawo shari’ar Musulunci a zamfara ba don biyan bukatun sa na siyasa.
A karshe dukkan magoya bayan APC a jihar Zamfara  muna sanar da al’ummar Najeriya cewar, ba ma tare da wadannan maganganu na Yariman Bakura da kuma yunkurin sa na dawowa da Bello Matawalle APC. Haka zalika dukkanmu munyi mubayi’a tareda ba da goyon baya ga Jagorancin jam’iyar APC a Jihar Zamfara karkashin jagora tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari.

Ra’ayi: Matasa Masu Kishin Jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *