Spread the love

Rufe kan iyakokin tudu na kasar nan waton Boda ya sanya an samu raguwar kalubalen tsaro da ake fama da shi a kasar nan

Ministan lamurran ‘Yansanda Muhammadu Maigari Dingyadi shi ne ya bayyana hakan a Sokoto lokacin da yake amsa tambayoyi ga Manema labarai a ranar Assabar din nan.

Ya bayyana cewa Jami’a Rundunar Yan sanda na Kasa a shirye suke  su karbi akalar yaki da mayakan Boko Haram daga hannun sojojin kasar nan don ganin samu wanzajjen zaman lafiya.

Wannan kuwa ya biyo bayan Shirin da ake kan yi na janye sojojin dake fagen daga a can Arewa maso gabascin kasar nan.

Ya ce shirye shiryen karbar ragwamar nanan ana ta yi  da masu Ruwa da tsaki ga wannan lamarin.

Ya Kara da cewa, da zarar aka kammala tattaunawa kan wannan lamarin, to Jami’a ‘Yan sanda za su tsunduma ga wannan aikin.

Ministan Haka Kuma ya maganta kan Shirin nan na gwamnonin kudanci kasar nan na Samar da wasu kayan aikin tsaro a yankunan su, inda yace sha’anin tsaro dai abu ne da yake a Hannun Gwamnatin Tarayya, duk da dai duk wani aiki na tallafawa Gwamnatin ga sha’anin tsaro to abu ne Mai kyau.

Muhammadu Maigari Dingyadi ya yi yabo da jinjina a kan kokarin wadannan Gwamnonin da kuma sauran masu Ruwa da tsaki ga lamurran tsaro, inda ya Kara da cewa, Amma fa kada a wuce makadi da rawa wurin taimakawa ga Samar da aikin tsaro.

Ministan ya ce samar da tsaro da kare mutane aikin gwamnatin tarayya ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *