Spread the love

Shugaban jam’iyar PDP na kasa Uche Secondus ya ce shugabannin jam’iya sun kai matsayar yin zanga-zanga a birnin Abuja kan hukuncin kotun koli da ta tsige Emeka Ihedioha kan kujerar Gwamna.

Ciyaman yana Magana a wurin taron majalisar zartarwar jam’iyar a hidikwatar jam’iyar dake Abuja ranar Juma’a data gabata ya ce manufar yin zanga-zangar domin a sanar da ‘yan Nijeriya rashin adalcin da aka yi wa PDP.

Secondus bai sanar da ranar da za a yi zanga-zangar ba, ya ce baiwa Hope kujerar gwamnan Imo rashin adalci ne, Allah ne kawai mai yin adalci amma dole su yi Magana in an yi masu rashin adalci.

A ranar Alhamis ne PDP ta yi kira da a sake duba hukuncin da aka yanke na jihar Imo da kuma kira da a cire Alkalin Alkalai Tanko Muhammad  daga matsayinsa don shi ne ya gurbata hukuncin.

PDP ta zargi fadar shugaban kasa da jam’iyar APC sun hada kai da kotun Koli  a karbe masu Gwamnonin jihohin Sokoto da Bauchi da Adamawa da kuma Benue.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *