Mukhtar Halliru Tambuwal Sokoto.

Ƙungiyar jinkan Alummah ta Alyatem charity initiative, sun kaiwa Makarantar Allo ta Modibbbo Abu da ke bayan Asibitin Maryam Abacha,tsofuwar kasuwa daukin kayan sanyi.
Shugaban kungiyar Malam Jabir Shinkafi ta bakin sakataren gudanar da ayukka Abdussalami Ibrahim Magawata, ya bayyana cewa sun amshi kiraye kirayen da ake yi ta yi na ataimakawa Almajirran, inda suka buda wani Asusu dan gunadar da wannan aikin,yace wannan farawa ce za su cigaba da gudanar da Shirin, yace sun Tara kudaden ne ta taimakon da suke samu ta Wani Asusun musamman da suka buda dan wannan aikin,da tallafin al-umnah da Kuma mambobin su da daidaikun mutane ke badawa Malam Bala da Modibbo Abu,sun yi godiya ga wannan Kungiyar, Almajirrai cikin farin ciki sunyi godiya da Addua ga duk Mai hannu a wannan aikin alkhairi.
An de raba kayan ne ga Almajirran maza da Mata da ke makarantar kusan su Dari.
Ita dai wannan kungiyar ,kungiya ce Mai zaman kanta, mainzimmar inganta rayuwar Mabukata,wadda wasu matasa, mafiyawancin su Dalibbai a manyan makarantu, suka daukar ma kansu aikin taimakawa Alummah musamman Yara marayu da sauran mabukata.
A lokacin rabo kayan akwai wasu mambobin kungiyar da suka hada da Halima Wasagu: Maitaimakiyar Shugaba, Ibrahim ja’o: Maajin kudi,
Asmau Sa’idu Yabo jamaiar kudi, Mustafa tukur illo ,Balkisu Tambuwal, Mukhtar A Haliru Tambuwal, da Musab Bodinga mambobin kungiyar.
A Yan kwanakkinnan Almajirrai a Sokoto,suna samun dauki daga Hukumomi, Kungiyoyin addini da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *