Spread the love

Mafiyawan Gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyar PDP ba su halarci taron da jam’iyar ta kira a birnin Abuja ba.

Kusan gwamna 11 ne ba su halarta ba, yayin da gwamna uku ne suka zo taron Gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da Adamawa Alhaji Ahmad Fintiri da Zamfara Bello Muhammad Matawalle da kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da wasu jigajiggan jam’iyar ‘yan kaɗan.

An shirya zaman ne kan hukuncin da kotin ƙoli ta yanke kan zaɓen Imo da aka soke zaɓen Emeka Ihedioha na jam’iyar PDP aka baiwa Hope dan APC.

A zaman tattaunawar za a yanke hukunci mataki na gaba da jam’iyar za ta ɗauka kan hukuncin na kotun ƙoli da sauran bayanai da za su shafi zaɓen 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *