Jam’iyar PDP a ranar Alhamis ta ƙalubalanci kwamitin alƙalan da babban jojin ƙasa Alƙali Tanko Muhammad ke jagoranta da suka  saurari ƙarar jihar Imo kan zaɓen 2019, da su janye kansu ga shari’ar Bauchi da Sokoto da Benue da kuma Adamawa.

PDP ta ce Alƙalan da suka yi shari’ar Imo sun nuna a Sauran shari’un dake gabansu  ba a tsakiya suke ba(suna da ɓangare kenan).

Jam’iyar ta gudanar da taron manema labarai a Abuja in da Shugaban jam’iyar PDP Uche Secondus ya ce jam’iyarsu ba za ta lamunce amshe damar mutanen Sokoto, Benue da Adamawa da Bauchi ba.

Ya yi kira ga Kotun ƙoli ta sake duba hukuncin da ta yanke a jihar Imo.

Ya kuma nemi Alƙali Tanko Muhammad da ‘yan uwan aikinsa Alƙalai da suka yi shari’ar Imo da su janye kansu ga sauran shari’un da suka rage wanda suka shafi PDP a kotun ƙoli. A cewarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *