Spread the love

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce ba za ta ƙyale duk gwamnan da ya ci kuɗin ƙananan hukumomi ba, Gwamna zai fuskanci shari’a bayan ya aje mulki ba da ɓata lokaci ba.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin Neja Delta Ita Enang ne ya sanar da hakan.

Ya sanar da Babban Akanta Janar ya riƙe bibiyar yanda ake kashe kuɗin a jihohi.

Ya ce gara ma gwamna ya sani zai fuskanci shari’a bayan ya ƙare mulkinsa.

Ya fahimci wasu sakatariyar mulkin ƙananan hukumomi ba su komai yayin da wasu cibiyoyin lafiya ba su aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *