Kungiyar jinkan Al-ummah da tallafawa Marayu, zawara da Mabukata watau ‘Alyatem Charity Initiative’ ta buɗe Asusun neman taimako dan samarwa Almajirrai da sauran mabukata Suturar Tufafin Sanyi, Hulluna da abin Lullubi (Bargo).
Mu hanzarta mu bada namu taimako dan tallafawa Almajirrai (maimakon mu tsaya gardama akan Almajirran )
Ga masu son bada na su taimakon suna iya sakawa awannan Asusun ajiyar mallakin kungiyar.
Sunan kungiyar
* Alyateem Charity Initiative*
Sunan banki
* Access Bank *
Lambar Akawon
Act Nomber * 0799494701*. Allah ya bada ikon Tallafawa.
Itadai wannan kungiyar halartacciya ce, tana da Rigista da hukumar tantance kungiyoyi da kamfunna Kamar yadda zaku gani a kasa.
Haka Kuma wannan kungiyar Wadda Malam Jabir Shinkafi ke jagoranta tanada mambobi da uwayen kungiya, ,Dr. Jabir Sani maihulla Sokoto,shine Shugaban kwamitin Amintattu,Yayin da Dr. Shadi Sabeh shine sakataren kwamitin Amintattu.
Ita wannan kungiyar jinkan Al-umnah bata Gwamnati ce ba,kuma ba ta siyasa ce ba, Ita de kungiyace ta addini, wadda wasu matasa, mafiyawancin su Dalibbai a manyan makarantu, wasu Kuma ma’aikatan gwamnati ne, suka daukar ma kansu aikin taimakawa Alummah musamman Yara marayu,Mata zawarawa da sauran mabukata.
Muna fatar Al-Ummar Musulmi da masu taimakawa su saka nasu jari dan girbar shi gobe kiyama. Malammai sunce “Annabi S.A.W yace shida Mai taimakawa maraye (ya daga yatsan sa) yace Kamar Haka muke gobe kiyama a Aljannah” Sun Kara cewa “Duk Wanda ya Gushewa wani bakin ciki , to a ranar Alkiya ma Allah zai Sanya shi a inuwar shi,ranar da babu wata inuwa sai tashi Mu hanzarta mu saka na mu taimakon Kar shaidan ya Hana mu, Sanya kalilan gobe kiyama ka girbe babban rabo.
Domin Karin bayani ana iya tuntubar Shugaban kungiyar Jabir Shinkafi, +2347031936501 ko Sakatariyar Kudi, Asma’u Yabo, +237036384145 maajin kudi Ibrahim Ja’o +2348139616485,Jami’in Gudanar da Ayukka Abdussalam Ibrahim Magawata +2347034274939 Ko Adreshi a makarantar Mus’ab bn Umar institute,Sama Road, Sokoto. Allah ya bada ikon taimakawa. Amin. Sanarwa daga Kwamitin Watsa Labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *