TAYA ZAN GANE CEWA MACCE MAI ADDINI CE?

Annabi (Saww) Ya Bada labari, a Cikin hadisi, Wanda da yawan mutane suka kuskure ainahin abinda hadisin ke magana akai.

Annabi (Saww) Yace, “Ana Auren Mata saboda abubuwa guda hudu; Abu na farko, Domin Kyawonta, Na biyu domin Danginta, na ukku Domin dukiyarta Sai Annabi (Saww) yace, na horeku da ku auri ma’abociya addini.

Wannan hadisin ba Annabi (Saww) yace, aje a auri macce Mai kyawo, ‘yar dangi, Mai dukiya ko dangantaka bane, a’a Annabi (Saww) Labari yake bayarwa domin kuwa, Indiyawa sune suke auren macce domin kyawonta, larabawa suke auren macce domin danginta, Yahudawa kuma domin kuddinta amma musulmi na kwarai (Wanda a kowace kabila za’a iya samunsa), shiyake auren macce domin Addininta.

A wani Hadisin ma da Ibn Majah Ya fitar Annabi (Saww) Cewa Yayi, “Kada ku auri mata saboda kyawon su, kyawonsu yana iya juyar da ita.( ta kasance mai girman kai.) Sai ya qara da cewa, “Kada ku auri mata saboda dukiyarsu: Ana sa ran dukiyarsu ta sanya su girman kai. Sai dai ku aure su saboda addini.”

Haka Wani mutumi ya je majalisin Safiyanu bn Uyaynah ya ce, “Ya Aba Muhammad ina fama da matata tana wulaqanta ni matuqar wukaqantawa.

Sai Safiyanu bn Uyaynah ya yi shiru kadan sannan ya ce, “Me yiwuwa ka aure ta ne saboda ka samu daukaka.” Sai mutumin ya ce, “Lallai haka ne. Sai ya ce, “Duk wanda ya auri mace saboda neman daukaka, to Allah zai qasqantar da shi. Wanda kuma ya auri mace saboda dukiya Allah zai jarabce shi da talauci. Wanda ya auri mace saboda addini Allah zai hada masa daukaka da dukiya da addini.

To taya mutum zai gane macce Mai addinice? (Addini shine tsoron Allah) domin ko fassarar Addini wasu sun kuskure, sun dauka Me ilimin qur’ani, hadisi dasauransu.

To shi tsoron Allah ba kamar yadda muke jin tsoron Maciji, wuta ko wani mutum bane wayannan abubuwa duk idan mutum ya samu saa zai iya yakarsu. Shi tsoron Allah a zuci yake Wanda kuma Ana gane mai tsoron Allah ta fuskoki da tawa, daga cikinsu akwai;

Neman Ilimin addini, Neman Ilimin addini na daga cikin abubuwan dake sanya a kwautatawa mutum zato akan yana tsoron Allah (Da inada lokaci danayi bayani Mai yawan gaske akan), amman dai munji neman Ilimi (musamman na addini), shine alama ta farko dake nuna mutum na tsoron Allah.

Abu na biyu, Yin ibada ba karamin Mai tsoron Allah bane ke dagewa dayin ibada, musamman a bacci DA kuma lokacin wasu hidindimu na yau DA kullum.

Abu na Ukku Abokantar mutanen Kirki, babu shakka duk Wanda ka gani tare da mutanen kirki, Ba mutanen banza ba to akwai bukatar ka kyautata masa zato domin zama tare da mutanen kirki da shiga abubuwa na addini yana daga manya manyan abubuwan da zaa tabbatar mutum nada tsoron Allah.

Tausayi DA zumunci suma suna ciki domin duk wadda ko Wanda kaga An yabawa akan zumunci tare da tausayi to wallahi wayannan halaye na daga cikin tsoron Allah.

Na taba samun labarin Cewa, Wata Yarinya ta ce ita faufau ba zata auri kowa na sai Mai tsoron Allah, In da yakai duk Wanda yazo Nemanta da aure sai ta bukaci yayi karatun Alqur’ani taji Idan har shi gwanine, Ita a tunaninta a haka zata samu Mai tsoron Allah.

Yake ‘yar uwa da Dan uwa hakika Baa gane Mai tsoron Allah ta bangaren karatu kawai, sai an binciki mu’amularsa da kuma abubuwan da mutum ya sanya a gaba.

Misali duk mutumen da KO matar da kaji ance babu abinda ta sanya a gaba sai sharholiyoyi da yawon biki babu lokacinyin komai na addini to kaima kasan babu tsoron Allah a tartare da Irin wayannan.

Alkherin wannan Rubutun Ina fatan samun lada ga Maina Adam Daga Gombe Shi ne yayi ta yi ta tuntunamin game da wannan.

Wannan rubutun Managarciya ta same shi ta hannun marubucin.

Jamilu Sani Rarah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *