Spread the love

Kotun ƙolin Nijeriya ta yi wa ɗimbin jama’a ba zata ganin yanda aka sa ran za a yanke shari’ar Kano bayan an kammala sauraren ɓangarorin mai ƙara da wanda ake ƙara, kwatsam bayan alƙalan sun gama shawara suka ayyana yanke hukunci sai wani sati 20 ga watan Junairun 2020 kenan.

Ɗan takarar Gwamna a jam’iyar PDP a Kano Abba Yusuf, na ƙalubalantar sake zaɓen gwamna Abdullahi Ganduje da aka yi a 9 ga watan Maris na 20.

Abba Yusuf ya ɗaukaka ƙara a kotun ƙoli biyo bayan nasarar da Ganduje ya samu a Tarabunal da kotun ɗaukaka ƙara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *