Spread the love

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi gargaɗi kan yadda jahilci ke ƙara yawa a Arewacin Nijeriya yana iya zama musibar da ba a iya tarewa a nan gaba.

Ya dubi yanda lamarin mahara yake a Katsina ya sanar a ƙarshen satin da ya gabata.

Masari ya koka kan yanda mahara ke ƙara yawa a cikin dajijjukan wani ɓangare na Arewa. Ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa da haɗari.

“Mafi yawansu ba su da ilmi na addini da zamani, muna da matsala a yanzu a daji muna tare da mutanen da ba su da kowane ilmi, ba su da ilmin addini ba su da na Boko, su ne ke faɗa da mu suna faɗa da al’umma”

“In ba mu tashi tsaye muka magance matsalar ba, abin da zai fito a cikin dajin, nan da shekara 20 in ka haɗa da abin da ke faruwa yanzu wannan wasar yara ne”.

Ya nuna akwai buƙatar gyaran ilmin furamare yanda za’a magance matsalar a daina haifar yara ba a kula da ilminsu.

Masari ya ce harkar almajirai ya kamata a duba ta a Katsina suna da kusan yaro dubu 996 da ba su zuwa makaranta suna yawo saman hanya, kamar yadda ƙididdigar majalisar ɗunkin duniya ta nuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *