Spread the love

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya yi kira ga magoya bayansa da daukacin mutanen jiha su yi hakuri biyo bayan dage sauraren shari’a da kotun koli ta yi kan kalubalantar zabensa da jam’iyar APC da dan takararta ke yi.

Gwamna Tambuwal haka ma ya yi kira ga mutane su fita batun jita-jitar da ake yadawa cewa dakatarwar an yi ta ne don a goyi bayan masu kara.

Kotun koli dake zamanta a Abuja ta dage zamanta a yau Litinin da safe zuwa gobe Talata in da aka sa ran za ta yanke hukuncin daukaka kara da aka sanya na kalubalnatar zaben Tambuwal da wasu gwamnoni shida masu ci.

Kotun ta sanar da dage zamanta a dalilin daya daga cikin alkalan ya kamu da rashin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *