Spread the love

Sojojin Nijeriya sun kashe mahara sama da 50 a maɓuyarsu a kusa da dajin Ruga cikin ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tsaro Ibrahim Ahmad Katsina ya faɗawa manema labarai yanda gwamnati ta ɗauki matsalar maharan da girma da dawo da tsaro ga harkar garkuwa da mutane.

Ya ce da ƙarfe ukun dare ne sojoji suka gano maɓuyar maharan a Jibiya kusan mutum 50 daga cikinsu aka kashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *