Spread the love

Gwamna Tambuwal ya karrama wakilan kungiyar Dalibbai musulmi,’MSSN’ na jihar sokoto da suka samu nasara a karo ukku jere da juna.

Daga Mukhtar Halliru Tambuwal Sokoto.

Gwamnan jihar sokoto Aminu Waziri Tambuwal matawallen Sokoto ya yi wa wakilin mssn na jihar sokoto goma ta Arziki bayan sun kai mai ziyarar kai mashi kyautukkan da suka samu a lokacin taron uwar kungiyar na yakkin Arewacin kasarnan da aka kammala a garin Kano.
Gwamna Tambuwal, Wanda ke cikin farin ciki,ya jinjinawa mambobin kungiyar na dagewa akan samun wanna nasara, ya bayyana anniyar gwamnatin sa na goyon bayan kungiyar a daukacin ayukkanta, Yayi Kira ga dalibban da su cigaaba da zama jekadu na gari da kuma kyawawan dabiu na gari.
Shugaban kungiyar na jihar sokoto Alhaji Abubakar Sadik Isa ya bayyanawa gwamna Tambuwal cewa sunje ne ofishin sa domin amsa gayyatar gwamnan da kai kyautukkan da wakilan kungiyar da suka wakilci sokoto suka samu shekarar ukku jere ,Shugaban ya bayyana cewa duka wannan nasarar da aka samu ta ta’allaka ne akan goyon bayan da gwamnan ke baiwa kungiyar, kana manufar gwamnatin Tambuwal na sanya dokar ta bace akan ilimi, ya fara haifar da Da mai ido, Alh. Sadik, ya bayyana cewa an fafata ne a fannonin Kaci kaci na Harshen Turanci da Larabci, Muhawara,Rubutun insha’I, Magana ga ban jama’a duk a cikin harsunan Turanci da Laranci,Wanda wannan jihar ta samu gagrumar Nasarar zama mafi samun Nasarori kolin a Jihohi sha tara na Arewacin kasar nan, ciki har Abuja da suka fafata, inda ya gabatar da daukacin kyautukkan ga gwamnan.
Gwamna Tambuwal ya bayyana alkawalin baiwa Rukunnan wakilan sokoto na shekara 2017, da suka yi nasara a jihar Jigawa, na shekarar 2018 a jihar katsina da na shekarar bara 2019 a Taraba, ko wanen su kyautar Naira miliyan biyu, ya kuma bada kudin cin abinci nan take ga wadanda suka je na Naira miliyan daya tare da alkawalin bada Mota sabuwa mai daukar mutum 18 da naira miliyan daya ga kungiyar jaha.
Taron ya samu halartar mukarranbayyen gwamnati,wasu shugabannin zartarwar kungiyar,mambobi da dalibbai maza da mata daga makarantinne Daban daban.
A karshe, angabatar da Addua da hotuna. Rubutawa Mukhtar A Haliru Tambuwal jamian hulda da jamaa na kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *