Spread the love

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce sama da malaman jami’a dubu 96 ne suka shiga cikin sabon tsarin biyan albashin tarayya na IPPIS.

Jami’o’i nada malamai kusan dubu 137,016 kuma dukansu ykmata su shiga cikin tsarin.

Ministar kuɗi Zainab Ahmad ce ta gitar da bayanin da kira ga ƙungiyar malamai ta ƙarfafi sauran malamai dubu 40,926 su shiga cikin tsarin.

Shugabannin ƙungiyar sun tattauna da shugaban ƙasa amma dai bayan kammala zaman an nuna kowa na saman bakarsa.

Samun fiye da rabin ‘yan ƙungiya su karɓi shirin na gwamnatin tarayya ba ƙaramin lahani ba ne ga duk wani yunkurin shugabannin ƙungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *