Spread the love

Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji uku da farar hula takwas a Monguno jihar Borno a ranar Talata data gabata.

Maharan na tare da motarsu mai ɗauke da abubuwan fashewa suka shiga cikin jerin gwanon motocin sojoji, wannan abun ya faru bayan kwana 10 da sojojin Chadi suka jaye daga taimakon Nijeriya ga yaƙar ISWAP kan iyakar Chadi da arewacin Borno.

An fahimci maharan sun ƙone wasu tanti sama da 300 sun kashe mutum takwas da raunata wasu mutane a Monguno kilomita 100 daga Maiduguri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *