Spread the love

A ƙalla fasinjoji 12 sun rasu a mummunan haɗarin mota a ƙauye jihar Kano wanda ya faru da midalin ƙarfe 10:30 na safen jiya Laraba.

Haɗarin na mota biyu ne kan hanyar ƙauyen Tsaida kusa da garin Gaya a ƙaramar hukumar Gaya.

Wani mstafiyi a saman hanyar zai je Azare jihar Bauchi ya ce msu taimako ne suka cire sauran waɗan da suka samu rauni daga cikin motar da ta fi buguwa.

Ya ce hatsarin ya samu ne tsaksnin mota bus mai ɗaukar mutum 18 da wata motar da ta rabu biyu.

Jami’i a babbar asibitin Gaya ya ce mutum 12 ne suka mutu ciki akwai mace ɗaya da yara biyu da da maza tara. Ya ƙara da cewar mutum 20 ne suka samu rauni a hatsarin.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗurra ta Kano Kabiru Daura ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ƙarin bayani sai daga baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *