Spread the love

FOMWAN RESHEN JIHAR SOKOTO SUN KAIWA WASU ALMAJIRRAI TALLAFIN KAYAN SANYI.

Daga Mukhtar Halliru Tambuwal.

Kungiyar Tarayyar Mata Musulmi ta kasa reshen jihar Sokoto (Fomwan) Da yammancin Ranar Larba 8/1/2020 Sun kaiwa Wasu Almajirran Makarantar Malam Bello Maizuma dake unguwar Illela, gabascin filin sukuwa akan titin maikahon Karo, dake cikin garin sokoto tallafin suturar kayan sanyi.
Shugaban Da’awa ta fomwan Hajiya Ikram Omar Bello ce da wasu mambobin fomwan suka rabawa Almajirran Tallafin,a gajeren Jawabin ta Hajiya Ikram tace sunje makarantar ne domin su raba kayan sanyi ga Dalibban ,tace “fomwan reshen jihar Sokoto tana aiwatar da ire iren wadannan ayukkan jinkan alummah”, tace sun lura a wannan yanayin kowa na bukatar Sanya suturar sanyi danbaiwa Jikin shi kariya,sun lura mafiyawancin Almajirran basuda kayan sanyi,wannan ne yasa mambobin kungiyar suka nemi kudin dan sayen tufafin da rabawa yaran, tayi Kiran yaran da su tsaya suyi karatu ,su Zama jekadun makarantar na gari maimakon yawace yawace barkatai,tace su zanka kula da tsaftar Jikin su da ta muhallin su,kana su zanka wanke tufafen,”idan sanyi ya wuce a wanke a a je har badi.
Wakilin Malam Bello Maizuma ,Malam Aminu Bello ne ya tarbe su,kana jayi godiya akan wannan tallafin.
Sama da Yara Dari ne suka amfana da tallafin.
Wasu da muka zanta da su ,sunyi godiya da Addua ga Fomwan reshen jihar Sokoto. Anyi Addua ta musamman a lokacin rabon kayan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *