Spread the love

Usman Abbas ya roki kotun shari’a dake zamanta a Magajin Gari a jihar Kaduna ta sanya Maryam Yusuf Nadabo macen da ya so ya aura da mahaifinta Yusuf Nadabo su mayar masa da sadakinsa.

Usman ya sanar da kotu cewa ya kashe dubu ɗari da goma (110,000) a ya gani yana so da sadaki da kayan wankin amarya, duka kuɗin ya miƙa su ne ga dangin Maryam.

Ya ce tun sanda aurensu shi da Maryam bai yiwu ba yakamata danhinta su mayar masa da kudinsa ya kashe dubu 10 a ya gani yana so da wasu dubu 60 na sadaki da dubu 40 na wankin amarya.

Ya ce ya yi tsammanin ɗaura aure bayan ya kammala wajibi sai ya yi tafiya bayan ya dawo ya fahimci dangantakar ta canja shi da Maryam.

Mahaifin yarinyar ya aminta da maganar Usman sai dai ya ce sadaki dubu 50 ne ba 60.

Yusuf ya ce sun yi yarjejeniya da mahaifin Usman yanda za a mayar da kuɗin ƙarshen wannan watan na Junairu.

Alƙali Murtala Nasiru ya ɗaukaka sauraren ƙarar zuwa 13 Junairu don kowa ya kawo shedunsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *