Spread the love

Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce dole ne zaben Nijeriya ya rika gudana babu tashin hankali, harkokin su tafi ba cin zarafi ana yi cikin mutuntawa, hakkin ‘yan sanda ne su ga hakan ya faru ina sa ran hakan ya faru a zabuka na kusa da za su faru don samar da cigaba.

Buhari ya yi wannan jawabin ne a jiya lokacin da ya tattauna da shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu da wau shugabannin hukumar tare da shugaban ‘yan sanda na kasa Mohammad Adamu a fadar shugaban kasa.

Shugaban kasa ya bayyana abin da ya sanya a gaba shi ne samar da tsari da zai baiwa masu zabe damar gudanar da zabe da duniya za ta gamsu da shi.

Hukumar zabe da ‘yan sanda sun yi alkawalin bin dokoki da zai sa shugaban kasa ya cimma burinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *