Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana kudirinsa na Sokoto ta cigaba da zuwa wasan kokuwa a shekarru masu yawa har a bayan mulkinsa.

Ya ce kun sani wanda na gada ya yi ta zuwa kasar nan kallon wasar duk shekara na rike wannan al’adar dafatar za ta dore.

Tambuwal ya yi kira ga gwamnonin Arewa su fito da wasanni al’ada domin raya al’adun da ake da su.

Gwamna Tambuwal ya yi wadan nan kalamai a wurin wasan kokuwa ta gargajiya karo na 41 da aka yi Maradi jamhuriyar Nijar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *