Spread the love

Jam’iyar APC a jihar Sokoto ta nemi sanin halin da kasafin kuɗin 2019 ya kwana ganin manyan aiyukkan da ke cikin kasafin ba a yi su ba kuma ba wani labari kansu na in da aka kwana da in da za a je.

APC sun yi wannan kalaman ne a wurin taron manema labarai da suka kira a hidikwatar jam’iyarsu a Sokoto.

“Lokacin da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana gaban majalisar dokoki domin gabatar da kasafin kuɗin da ya yi wa laƙabi da cewa ‘kasafin kuɗi don cigaban tattalin arziki da walwala wanda kowa zai morewa’ bukin ya zo ya wuce kamar ruwan faƙo jama’ar jihar Sokoto sun san cewa ‘yar gidan jiya ne an faɗa ne kawai, ba aikin za a yi ba, iyakar labarin gidajen watsa labarai da jaridu. A duk shekara haka ake yi” a cewar Isah Sadik Achida da yake yi wa manema labarai bayani.

Ya ce Tambuwal ya saɓa wa yadda ake yi a duniya ba jawo ruhe da ya yi a kasafi ba.

Achida ya kawo wasu muhimman aiyukka biyar da gwamnatin ta aminta za ta yi a shekarar da ta gabata amma ba a yi ba har yanzu irinsu gyaran hanyar filin jirgi da za a kashewa miliyan 548 da ƙarin gine-gine a harabar ɗakin taro na ƙasa kan miliyan 128 da ginawa da samar da kayan aiki a cibiyar binciken curita kan naira biliyan biyu da samar da littafai a kwalejin ilmi ta shehu Shagari kan miliyan 96.7 da yin gyare-gyare kwalejin ƙere-ƙere dake Bafarawa kan miliyan 98.83.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *