Spread the love

Na Gwammace Na Sadaukar Da Rayuwata Wajen Hidimtawa Talakawa Maimakon Na Bar Su Cikin Wahala, na tsira da raina.

Gwamna Zulum ya kara da cewa “abinda na fi tsoro shine na tsaya a gaban Allah bayan na ci amanar al’ummar jihar Borno.

“Na fito daga zuri’ar da ba su da hali, na zo na fara aikin tukin mota amatsayin direba duk don na samu kudin biyan makaranta, har Allah ya sa na zama Farfesa. Don haka ni na kowa ne.

“Ina da tabbacin cewa idan Allah ya kaddara zan mutu a yau babu wanda ya isa ya hana. Kamar yadda na rantse da kur’ani, zan ci gaba da kyautatawa al’ummata”, cewar Gwamna Babagana Umara Zulum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *