Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jinjinawa Gwamnan Rivers, Nyesom Wike kan nasarorin da ya samu.

Gwamnan ya yi Magana ne  a sabuwar shekara ta 2020 na jihar Rivers a gidan gwamnatin jihar dake  Port Harcourt a ranar Laraba da dare, kamar yadda jaridar The Nation ta labarta.

Tambuwal ya yabawa mutanen jihar  Rivers kan tsayin dakar da suka yi suka kare zabinsu suka kare duk wani yunkuri na yi masu magudi a zaben gwamna na 2019 da ya gabata.

“Mun yabawa al’ummar Rivers kan tsayin daka su kare zabinsu a 2019, kun tsayawa dimukaradiya kuma kun tsayawa jihar Rivers.

“Muna biye da abin da ya faru kuma mun rike yanda al’ummar Rivers suka hadu wurin kare dimuukuradiyya.” A cewar Tambuwal.

Gwamnan ya ce Shi  Major Mustaha da ya yi yunkurin mirde zaben Rivers shi ne aka shigo da shi Sokoto bayan da aka ayyana zabe bai kammala ba, duk da hakan bai samu nasara ba.

Ya ce Nijeriya za ta cigaba da zama da karfinta matukar shugabanni suka cigaba da yin kyakkyawan shugabanci, “In kana maganar gwamnati da aiwatar da aiki a fadin Nijeriya sunan Gwamna  Nyesom Ezenwo Wike zai ci gaba da zama sama.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *