Spread the love

Gwamnan Borno Babagana Zulum ranar bukin sabuwar shekara ya buɗe aiyukka biyar da ya fara cikin wata shidda, sannan ya duba wasu aiyukka da ake kan aiwatarwa a ƙaramar hukumar Hawul dake kudancin Borno.

Gwamnan ya share kwana uku cikin Gwoza bai dawo Maidugiri ba ya ƙaddamar da aiyukka da rabon abinci ga ‘yan gudun hijira sannan ya tafi Hawul ranar sabuwar shekara.

Ya bude babbar asibiti mai daukar gado 100 a garin Azare da wata ƙaramar asibiti mai ɗaukar gado 40 a Kwajjafa, da wata cibiyar koyar da sana’a.

Sannan ya bude makarantar Firamare da karamin wurin duba msras lafiya a Kwayabura a Hawul ya duba aikin gina babbar Makarantar Firamari da ginin fadar uban ƙasar Kwajjafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *