Spread the love

Jam’iyar PDP a Nijeriya sun nemi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya janye kalamansa na cewa zai ja baya a 2023, kalamar na cikin saƙonsa na barka da sabuwar shekara.

PDP sun yi bayanin ne ta hannun sakataren yaɗa labarai Kola Ologbodiyan ya ce a tsarin dokar ƙasa Buhari da jam’iyyarsa ta APC ba su da wata mafita da ta wuce barin mulki in wa’adinsa ya cika.

‘Yan adawar sun nuna kamar Buhari yana nuna akwai yanda za a yi ya wuce 2023 in da dokar ƙasa ba ta yarda da hakan ba, tun da an zaɓe shi sau biyu zai bar ofis a 2023.

Sun bayyana tarihi ya ajiye waɗan da suka so sanya ƙasar cikin ruɗu, ‘yan ƙasa nason wuce wurin ba wai su tsaya yamaɗiɗin wannan ba.

PDP ta jefar da saƙon Buhari na sabuwar shekara saƙon bai nuna akwai sa ran wani abu na alfanu tafe ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *