Spread the love

Matashi dan shekara 20 mai suna Laulo Isa ya yi wa wata mata tsohuwa mai shekara 54 Mary Okereke fyade ta mutu a Ungwulangwu cikin karamar hukumar Ohaozara jihar Ebonyi.

Matashin ya ce sau daya ya sadu da ita kafin ta bar duniya.

Ya ce yana cikin magagin Giya ne da ya sha abin da ya kai shi ga neman matar bayacikin hankalinsa.

Laulo ya yi magana da manema labarai bayan da ‘yan sanda suka gabatar da shi a hidikwarsu dake Abakaliki ya ce ba shi da wani shiri na yi wa matar fyade, zagin shi da ta yi ne bayan ta ki aminta da neman ya sadu da ita ne, ya fusata shi ya yi mata wannan karan aiki.

Matashin ya yi nadamar abin da ya aikata ya ce baya cikin hayacinsa a lokacin da yi mata fyade.

Matashin dan jihar Nasarawa ne ya tafi yin aiki ne a jihar Ebonyi ya ce a ranar da abin ya faru ya sha Giya sosai ya bugu sai ya ga mace saman titi da dare tana tafiya, sai ya neme ta daga nan ta rika zaginsa.

Ya ce ana haka suka rika zagin junansu shi da ita nan take ya cukumeta ta yi kokarin fizge jikinta ta kasa, a lokacin shi a buge yake a haka ya kai ta kasa, sai da wani mutum ya zo ya haska su da fitilar hannun sannan ya tashi ya gudu.

“Na ji kamar na sadu da ita sau daya, ban ji dadin abin da na aikata ba kan haka ina ma in mutu, ina son in mutu, ban taba aikata irin wannan abun ba tun san da Allah ya halicce ni a duniya, ina neman a yafe ni.”

Kwamishinan ‘yan sanda Awotunde Awosola ya ce wanda ake zargin za a ki shi kotu kan laifin da ya aikata.

Ya ce abin rashin jin dadi matar ta rasa ranta a lokacin wannan abun, gawar matar yana asibiti yanzu haka abin ya faru ne a 28 Disamban 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *