Spread the love

Hukumar Hisbah a jihar Zamfara sun kama Dan sanda da wasu mata uku kan zargin suna aika abin da baikamata ba a tsarin rayuwar musulmai a Otal cikin birnin Gusau.

Shugaban hukumar Dakta Atiku Zawiyya ne ya fadi hakan a lokacin da yake gabatar da masu laifin hidikwatar hukumar a ranar Litinin data gabata.

Ya ce Dan sandan yana aiki ne da babban Ofishin ‘yan sanda na Gusau, sun kama shi tare da mace uku a daki daya na Otal ana zarginsu da aikata abin da shari’a ta hana(masha’a).

Zawiyya ya ce a binciken da hukumar Hisbah ta gudanar ta gano daya daga cikin matan ‘yan jihar Kaduna ce, biyu matan ‘yan gida guda ne a Zamfara.

Shugaban ya ce hukumarsa ta gargadi masu Otal din lokutta da dama kan su bar a jiye irin wadan nan mutane amma sun ki bin ka’idojin da jihar ta gindaya ga masu sana’ar Otal.

Manajan Otal din ma hukumar ta kama shi za a gurfar da wadan da ake tuhuma da zaran an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *