Spread the love

San Turakin Dutse Alhaji Mustapha Sule Lamido tare da Gwamnan Jihar Sokoto Rt. Hon Aminu Waziri Tambuwal suna kan hanyarsu ta zuwa birnin Port Harcourt na Jihar Rivers, don tattaunawa ta musamman tare da Gwamnan Jihar Rivers Barr. Nyesom Wike.

Wasu na hasadhen tattaunawar nada nasaba da harkokin da suka sanya gaba musamman ganin yanda jam’iyarsu ta PDP ta sanar da cewa za ta shiga neman ɗan takara ɗaya tilo da zai yi wa jam’iyar takara.

Tambuwal da Wike suna da fahimtar siyasa ana ganin tasu ta zo ɗaya ba a mamakin ganin sun keɓe don tattauna abubuwan da suka shafi ƙasa da siyasa.

Tijjani Abdullahi Kila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *