Spread the love

Mahara a daren ranar Lahadi sun kai farmaki a gidan ɗan kasuwa Alhaji Tasi’u Wali a garin Jibiya ta jihar Katsina sun kashe mutum ɗaya da yin garkuwa da mutum uku.

Mutanen da aka sace matar ɗan kasuwan Asma’u Tasi’u tare ɗanta mai shekara ɗaya da sakatarensa Abu Abu.

Wali wanda yake Sardaunan Jibiya majiyar ta sanarwa daily trust maharan sun zo gidan ne da misalin ƙarfe 8:30 suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi.

Mai magana da rundunar ‘yan sanda SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce maharan sun harbi wani Ibrahim Usman an kai shi asibiti daga baya ya rasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *