Spread the love

aishabasheer2017@gmail.com
A’isha Bashir tambuwal


Masu bibiyar shafin mu na Girke-Girke ina muku lale marhabin da sake haɗuwarmu da ku , a yau dai zamu sarrafa muku samosa.

SAMOSA

*Kayan haɗi


*Flour
*Nama
*Cabbage
*Carrot
*Attarugu
*Albasa
*Curry
*Maggi
*Gishiri
*Mai
*Kwai
*Baking powder

Haɗawa.
Da farko za ki wanke nama ki gyara shi ki ɗora a wuta ki saka magi da ɗan gishiri kaɗan da curry ki yanka albasa sosai idan ya yi laushi sai a daka shi tare da attarugu ki maida shi kamar dambun nama,sai ki ɗauko carrot da cabbage dinki ki gogasu sai ki soya su bayan kin gama wannan sai ki ajiye a gefenki, ki tankaɗe flour ki ɗan zuba gishiri da bakin powder kaɗan ki zuba mai da ruwa ki kwaɓa karki bari kwabin yayi ruwa fa yayi laushi sosai sai ki dinga murzawa yayi faɗi sai ki kawo wannan haɗin da kika ajiye a gefe ki dinga zubawa ki dinga ninke shi kamar ninkin dankwali ki saka a mai ki soya.

Bayan ya soyu ki cire abinki sai ci kawai yanda kike so.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *