Spread the love

Daga Mukhtar Halliru Tambuwal Sokoto.

Tun bayan da Gwamna Tambuwal ya zabo matashin Kuma ya yi Mai mashawarci akan lamurran matasan jihar Sokoto, Naradden Harande Mahe mafiyawancin matasa sun yi na’am da wannan nadin,da yimai addua da fatar matasan suma za’a dama da su,bayan gudun mawar da suka bada na kafa gwamnatin,duk da har wadan da bayan jamiyyar daya ba,sun yi murna Kuma sun taya matashin murna ,cikin Yan kwanakki kalilan da tarewar sa a sabon ofishin sa, Haka ta fara cimma ruwa,domin kuwa Hon. Nuraddeen Harande, ya fito da wani shiri na zaburadda dubban matasa domin yin ayukkan Sanya Kai, a fannoni daban daban da zimmar magance zaman kashe wando,habaka tattalin Arziki, a fannoni lafiya,Ilimi,tsaftace muhalli, tsaro da sauran su. Shirin Mai suna ‘Himma Matasa’ (Youths Volunteers Network) zuwa yanzu ga cikakken bayanin yadda zaa amfana da Shirin daga ofishin sa,
Ayi karatu lafiya CIKAKKEN BAYANI AKAN SHIRIN HIMMA-MATASA–)

Wanda Ofishin maiba gwamna shawara kan matasa yafito dashi…….

Shirin Himma matasa shirine da aka fito dashi a karkashin ofishin mai baiwa Gwamna shawara akan lamurran matasa na jihar sokoto Hon. Nuraddeen Harande Mahe wannan shirin anfito dashi da Zimmar fadakar da matasa nasu Rungumi Ayukkan taimakon kashin kai da sadaukarwa a cikin Al’umma.

Shiri ne da zai chanja tunanin matasanmu akan bata lokuttansu da janyo hankali na Amfanarda Al’umnominsu don Tserewa tsara musamman in aka kwatanta da takwarorin mu matasa na wasu sassan kudancin kasarnan.

Hakama wannan shirin yasamu amsa sunanshi na #HimmaMatasa ne don zaburar da matasan jihar nan dasu zama masu amfanar da Al’umnominsu ta hanya aikin kashin kai da sadaukarwa musamman bangarorin ilmi , lafiya , tsaftar muhalli , da wasu sauran ayukkan jinkan Jama’a hakika wannan shirin zai sakawa matasa kishi da saudakarwa ga Al’ummominsu dabam- daban .

Har’ilayau shirin ya kunshi jinsin maza da mata matasa don hada hannun da karfe don shiga kowane lungu da sako na wannan jihar tamu.

Babu siyasa a cikin wannnan shirin don shirine na kowane matashi dan jiha ya shigo a tafiyar da wannan aikin Alheri tareda shi .

(YADDA TSARIN ZAI KASANCE)

Matasa masu Zimmar bada gudunmuwa ga cigaban Al ummominsu.

~ BANGAREN ILIMI:- Matasa Masu Takardun

Diploma, #NCE, #Degree

Zasu taimaka a cikin makarantun yankinsu don cigaban Al’umma , ta bangaren daukar koyarda darussa da kuma kikkiro Extra lesson wato aji akan koyarwa ta musamman ga dalibbanmu da yaranmu a cikin Al umma.

~BANGAREN LAFIYA:- Matasa
Masu takardun shaidar karatun lafiya da suma suka kammala kan iya bayarda tasu gudunmuwa ga #Asibitocin_yankunansu don aikin kashin kai tareda sadaukarwa ga marasa lafiya.

~ BANGAREN TSAFTAR MUHALLI:-
Tabbas wannan aiki yanada muhimmancin gaske a cikin Al’umma don ko babu komi tsafta abin cikon Addinice , muhalli mai tsafta abin alfaharin kowace irin Al’umma ne , wannan bangaren kansa aikine na kowa da kowa musamman matasa masu jini a jika don sa kai da aikin kashin da sadaukarwa don sharewa da tsaftace muhallanmu a lokaci zuwa lokaci .

      (BANGAREN AYYUKAN JINKAN Al'UMMA)

Matashi mai kishin yankinsa kan iya shiga ayi ayukkan gayya dashi a matsayin gudunmuwarsa ga cigaban yankinsu .

Bayani akan shawarwari ga wasu batagarin matasa don gyara hali.

Kafa kwamitin saka ido da zai kunshi matasa ga shiga da fice a yankunansu don tabbatarda yanayin tsaro.

           (MATAKAN WAN'NAN SHIRIN SUNE)
 1. Kafa babban kwamitin Gudanarwa na jiha a karkashin jagorancin Hon. Nuraddeen Harande Mahe S.A Youth Matters.
 2. Tabbatarda Jagororin kananan hukumomi na wannan shirin #HimmaMatasa Wato L.G.A Coordinators .
 3. Tabbatarda jagororin Mazabu na kowace karamar hukuma na #HimmaMatasa (Ward Coordinator)

Wannan shiri da fatan zai karade ko ina a wannan jihar tamu ta sokoto, kuma tabbas muna kyautata zaton matasa million daya zasu Rungumi wannan shirin #HimmaMatasa tareda aiwatarda ayukkan sadaukarwa a yankunansu ta hanyar yin Rijista a ofishin mai baiwa Gwamna shawara akan lamurran matasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *