Spread the love


Daga Mukhtar Halliru Tambuwal Sokoto.

Kungiyar Dalibbai musulmi reshen jihar Sokoto,Mssn karkashin jagorancin Shugaba na jiha Alhaji Abubakar Sadik Isa, a Karo na ukku Jere da juna suna samun gagarumar nasarar samun kyautukka Wanda uwar kungiyar (A-Zone ) ke shiryawa a duk shekara ga dalibbai na yankin Arewa, samun wadannan nasarorin a karkashin jagorancin Shugaban da mataimakatan sa, babbar nasara ce ga Dalibban jihar Sokoto da ma mambobi da shuwagannin kungiyar da alummar jihar Sokoto baki daya.
A ranar larba 25/12/2019 aka gudanar da taron rufe kwasdin musulunci na IVC Karo na 77, Mai taken “Rawar da Dalibbai musulmi za su taka wajen kawo karshen kalubale da tattalin Arziki fuskanta” Wanda ya samu halartar maimartaba sarkin musulmi da sauran manyan baki,kuma Kungiyar Mssn ta sokoto sun karbi kyauta mafi daraja wadda sarkin kano muhammad sanusi 11 ya mikawa shugaba na jihar Sokoto,tare da karbar sauran kyautukka daban daban a sauran bangarorin da wakilan jihar Sokoto suka fafata a watan Tara a jihar Taraba, Jinkadan da isowar tawagar jihar Sokoto, shugaban ya bayyana jindadin sa akan wannan nasarar inda ya bayyana cewa bayan samun gagarumar Nasarar da kungiyar ta samu ta jiha ,sun Kuma karbo kyautukka har guda Goma Shadaya, yace sama da mutum dari ukku ne suka halarci taron na bana , daga manyan makarantu,kanani da islamiyoyi..yayi godiya akan goyon bayan da suke samu ga gwamnatin jihar sokoto,Majalisar Mai martaba sarkin musulmi,sauran kungiyoyin addini,malammai da Tsofaffin shugabannin kungiyar.
Idan baku mantaba a bara ne jihar sokoto ta dauki bakuncin taron inda Gwamna Tambuwal yayi masu goma ta Arziki ta hanyar rabawa dalibban sama da miliyan arbain ta basu naira Dubu goma goma na Kudin mota da yin kananin sanaoi.
Wasu da suka halarci taron sun nuna jin dadin su akan samun halarta . “Naji dadin zuwa IVC,Kuma na Karu sosai” inji wata daliba Maryam Magaji daga makarantar G.G.D.S.S Maberar Mujaya, Shima wani mahaifi da yazo daukar Yaran shi mai suna Malam Abubakar Yusuf Yeldu yace “Nasan muhimmancin zuwa IVC dan naje tun shekarar 1981,ayukkan da mssn keyi a makarantu na tarbiyatar da yaran mu abune Mai kyau,musamman a makarantinne gwamnatin tarayya da ake samun kalubale” Shima Nuhu sambo daga mssn ta yankin yabo ya nunajin dadin sa na samun kyautukka da akayi.
A shekara maizuwa zaayi taron IVC ne a Jihar Taraba, dan haka zamu fara shiri tunda wuri inji daya daga cikin mambobin mssn na jiha Malam murtala Aminu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *