Martani: Badaƙalar Albashi a Jihar Zamfara

Martani: Badaƙalar Albashi a Jihar Zamfara: Maganar da Kwamishinan Kuɗi Rabiu Garba Gusau ya wallafa akan Tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari da Tsohon Kwamishinan Kuɗi Muktar Idris ba gaskiya ba ne.

A wani rohoton ƙarya da Kwamishinan kuɗi na jihar Zamfara ya wallafa ga manema labarai kwana daya da ya gabata kan matsalolin albashi da badaƙalolin kudin albashi a Jihar zamfara ya kara tabbatar da cewar gwamnatin zamfara ta sharara karya ne tsagaronta akan tsoho Gwamna Abdul’aziz Yari da Tsohon Kwamishinan Kuɗi Alhaji Mukhtar Idris.

Babu wani shiri na badakalar kuɗi wanda tsohuwar gwamnatin Abdul’aziz Yari ta aiwatar a cikin shekaru takwas na mulkinsa kamar yanda kwamishinan kuɗi na jihar zamfara Alhaji Rabiu Garba Gusau ya bayyanawa manema labarrai, domin kuwa a Tarihin jihar Zamfara babu wata gwamnati wadda ta shuɗe da dukkan tsawon lokacin gwamnatin doka ce sai anyi bayani tareda bincike na kwakwaf akan yanda albashin ma’aikatan Zamfara ke gudana sai gwamnatin tsohon gwamna Abdulaziz Yari don tabbatarda gaskiya.

A bayaninsa na kuskure Kwamishinan kuɗi Rabiu Garba Gusau ya bayyana cewar ma’aikata kusan 4,972 ne ake biya albashi ba bisa ka’ida ba lokacin gwamnatin Abdul’aziz Yari wanda kowane wata suke lakume kusan miliyan 216. Muna kalubalantar Kwamishinan Kuɗii da dukkan gwamnatin jihar Zamfara da su wallafawa duniya sunayen wadannan ma’aikata na bugi da suke magana, su wallafa asusun bankinsu da ake biyansu wadannan kudade kowane wata, su bayyana karkashin wace ma’aikata ce aka biyansu kudin, kuma su bayyana a karkashin wace hukuma ake wannan badakalar albashi da yawan kuddin suka cimma miliyan 216.

Akwai mamaki ga irin wanda yake rike da mukamin kwamishinan kuɗi saboda kokarin farantawa mai gidansa Gwamna Bello Matawalle ya yi ikirari da bayyana cewar wadannan badakalar duka an yi su ne da sanin Tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari da Tsohon Kwamishina Mukhtar Idris, ko kuma karkashin kulawarsu aka aiwatar.

Inda zaka kara gane cewar magana ce kawai wadda ba ta da tushe balle makama kwamishinan kuɗi Rabiu Garba Gusau yake yadawa akan tsohon Gwamna da kwamishinansa shi ne kan maganar cewar a lokacin gwamna Yari wasu mutane ana biyansu albashinsu kowane wata duk da ba ma’aikata ba ne, da kuma wadan da ake biya albashi biyu a wata, harma wai da ma’aikata wadanda ba sunansu a jerin ma’aikata amma gwamna Abdulaziz Yari yasa ana biyansu kowane wata ta hannun shugaban ma’aikata. Hakika Mutum idan yana son biyan buƙata, to tabbas zai iya bayyana komai don samun duniya da wani matsayi a cikinta, amma tabbas mutanen Zamfara da sauran al’ummar Najeriya ba mahaukata ba ne da zasu iya bata lokacinsu wajen yarda da irin wannan zancen. Babu wata gwamnati da zata iya gudana da irin wannan badakalolin musamman irin gwamnatin zamfara.

Duk wannan kame kame da karya ce karya ce wanda Kwamishinan Kuɗi Rabiu Garba Gusau ke yi, ya riga ya fahimci irin matsaloli wanda ya jefa jihar Zamfara a ciki yanzu, musamman a bangaren biyan albashin ma’aikata da bangaren habaka tattalin arzikin jihar da yawan tulin bashin bankuna akan gwamnati da kuma yanda ya jefa daruruwan mutanen Zamfara cikin bala’i na rashin albashi da abun dogaronsu na albashi da sunan ma’aikatan bugi.

Kila Kwamishinan kuɗi Rabiu Garba Gusau baya da masaniya akan cewar a jihar Zamfara yanzu haka kusan Kananan hukumomi shida ne ba su da manyan bankuna na biyan albashi, don haka mafi yawan masu karbar albashin a wannan yankunan suna amfani da wuraren aje kudade da tattarawa na jama’a wanda ake kira “Community Banking”, don samun albashinsu, ba wani asusun ajiya ko lambar BVM da irinsu za su iya gabatarwa ga gwamnati. Amma saboda da rashin sanin makamar aiki dukkan wadannan bayin Allah, Kwamishinan Kuɗi ya jefa su a cikin kuncin rayuwa na rashin albashinsu da abunda za su ciyar da iyalansu. Ta ya a hakan za’ayi tunanin samun zaman lafiya a Zamfara bayan mafiyawan wadannan da ake rikema albashi matasa ne da zasu iya bin wata mummunar hanyar wajen neman abunci da kudi tunda gwamnati ta rikemasu hakkokinsu.

  • Daga karshe muna kara kalubalantar Kwamishinan kuɗi Rabiu Garba Gusau da ma gwamnatin jihar Zamfara da su gabatarda hujjojinsu na wannan labarin da suke yadawa ga al’umma, wanda muka ɗauka ɓatanci ne ga mutane biyu masu daraja tsohon Gwamnan Abdul’aziz Yari da Kwamishinansa Mukhtar Idaris (Kogunan Zamfara).

Ra’ayi: Matasa Masu Kishin Jihar Zamfara.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *