Spread the love

Ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto Honarabul Isa Harisu Kebbe, mai waƙiltar ƙaramar hukumar Keɓɓe ya rasu a yau ranar Litinin.

Margayin ya yanke jiki ya faɗi a zauren majalisa in da nan take aka samu ya rasu.

Isa Harisu ɗan siyasa ne mai ƙwazo ya riƙe muƙamai da dama a gwamnatin jihar Sokoto kafin ya shiga zauren majalisa, ƙwarewarsa a harkar mulki ya sanya jam’iyarsa ta APC ta nemi ya tsaya takarar kujerar mataimakin Kakakin majalisar dokokin jiha in da ya sha ƙasa hannun wanda ke sama yanzu ɗan PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *