Spread the love

Kakakin majalisar dokoki Aminu Muhammad Manya Achida ya ce ‘yan majalisar dokoki na jam’iyar APC a jihar Sokoto kansu a haɗe yake kuma suna tare da jam’iyarsu a wurin gudanar da aiyukkan majalisa.

Kakakin ya faɗi haka ne a lokacin da ya jagoranci ‘yan majalisar 16 wurin kai gaisuwar girma ga shugabannin jam’iyar APC na Sokoto.

Manya Achida ya ce kanmu haɗe yake biyayyarsu ga jam’iya tana nan, sun kawo gaisuwar ne don ƙara ƙarfafa jam’iyar da yin zumunci dukansu abu guda ne suna aiki da shawara guda a majalisar dokoki.

Kakaki ya jinjinawa jagororin jam’iyarsa kan halin dattako da suka nuna bayan zaɓensu.

Shugaban jam’iya a jihar Sokoto Alhaji Isa Sadiƙ Achida ya ce ziyarar ta shiga kundin tarihi sannan ‘yan majalisa su ɗauki shugabannin jam’iya a jiha da matakin ƙaramar hukuma su yi tafiya tare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *