Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sanya hannu ga kasafin kuɗin shekarar 2020 na kuɗi sama da biliyan 202, in da ya zama doka.

Ya jinjinawa majalisar dokokin kan hanzarta ƙare aikin cikin sati uku daidai da tsarin majalisar ɗunkin duniya.

Tambuwal ya faɗi haka a lokacin da yake rattaba hannu ga ƙudurin a zauren gidan gwamnatin Sokoto.

Ya fahimci majalisar duk da tana ƙarƙashin jagorancin APC kuma su ne masu rinjaye duk da haka suna ba gwamnati goyon baya don ta yi wa jama’ar Sokoto aiki, ba za a yi wasa da damar ba.

Ya tabbatar majalisar zartarwa za ta yi aiki tare da ‘yan majalisar don tabbatar da an aiwatar da kasafin yanda yakamata.

Kakakin majalisa Aminu Manya Achida ya ce tabbatar za su cigaba ba da goyon baya ga shiraruwan gwamnati na smfanin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *