Spread the love

Mai tallafawa Editan Managarciya Kwamared Bello Sambo Bazza ya Angwance a jiya Assabar.

An daura auren ne bayan biyan sadaki dubu 50 kasa ba bashi ba, a unguwar Gidan Dare kan hanyar Zamau gidan malam Mika’ilu Dan-Baba da misalin karfe 10 na safe.

Daurin auren ya samu halartar dimbin jama’a ‘yan uwa da abokan arziki da masu gidajen angon, cikin manyan mutanen da suka shedi daurin auren akwai kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto Alhaji Aminu Muhammad Manya Achida da masu taimakawa na musamman ga Gwamnan Sokoto Alhaji Yusuf Dingyadi da Alhaji Kabiru Assada da sauransu.

Ganin yanda Matallafin Editan Managarciya yake mutum ne mai jama’a ba a yi mamakin yanda aka samu ambaliyar mutane a wurin daurin aurensa ba.

Tuni Amarya Ummu Mika’ilu ta tare a gidan mijinta, da fatar nan gaba kadan dukkan masu yi wa ma’aurata fatar alheri za su dawo domin shedar zanen sunan abin da Allah zai albarka ce su da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *